Magoya bayan Gbagbo sun yi zanga-zanga

Magoya bayan Gbagbo Hakkin mallakar hoto AFP

Daruruwan magoya bayan tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo, sun yi zanga-zanga a gaban Kotunan Munanan Laifuka ta Duniya a birnin Hague. Masu zanga-zangar da ke sanye da riguna da aka rubuta "Babu Gbagbo ba zaman lafiya", sun yi korafi a kan yadda aka tasa keyar tsohon shugaban zuwa kotun a watan jiya.

Gbagbo ya kasance shugaba na farko da ya bayyana a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniyar.

Ana tuhumar sa ne da laifukan da suka jibanci zubda jinin da ya biyo bayan zabukan da aka yi a kasar sa ta Ivory Coast.

Sai dai ya ce gurfanarwar tasa ta keta doka.

Mutane kusan dubu uku ne dai aka kashe a rikin siyasar kasar ta Ivory Coast, bayan Laurent Gbagbo, ya ki mika mulki ga Alasane Ouattara wanda ya lashe zaben da aka yi a kasar.

Karin bayani