Mutanen da sukai fama da cutar Kwalara a Haiti na bukatar diyya

Cutar Kwalara a Haiti Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana bukatar diyya ga wadanda sukai fama da Kwalara a Haiti

Dubun-dubatar jama'a ne suka gudanar da zanga-zanga a Kasar Haiti, suna bukatar majalisar dinkin duniya ta biya kudade a matsayin diyya ga mutanen da cutar kwalara ta shafa.

Masu zanga-zangar a garin St. Marc sun ce, sojojin kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya ne suka shigar da cutar zuwa Haiti, abinda ya haifar da annobar da ta kashe kusan mutane dubu bakwai.

Masu zanga-zangar na son majalisar dinkin duniya ta biya dala dubu dari a matsayin diyya ga duk mutum daya da ya rasa ransa.

Majalisar dinkin duniya ta ce akwai yiwuwar sojojin kasar Nepal ne suka yi sanadiyyar barkewar cutar, sai dai ta ce babu wani binciken kimiyya da ya tabbatar da hakan.

Karin bayani