Ana ci gaba da zanga-zanga a Russia

Hakkin mallakar hoto Reuters

Dubun-dubatar mutane a duk fadin Russia sun yi zanga-zanga suna kiran a sake yin zaben majalisar dokoki da aka yi a karshen makon jiya, wanda hukumomi suka ce jam'iyyar Hadaddiyar Russia ce da ke mulkin kasar ta lashe zaben.

Masu zanga-zangar na daga tutuci suna cewa, ''Putin tsuka ne!''; ''Putin tsutsa ne!'' Zanga-zangar dai ita ce mafi girma Moscow.

A birnin St Petersburg, an samu hatsaniya yayinda 'yan sanda suka yi kokarin cafke wasu masu zanga zangar. A cewar daya daga cikin daliban da ke zanga zangar babbar manufar wannan zanga zangar itace soke zaben da aka gudanar a kasar.

Zanga zangar dai ba a Birnin Moscow kawai ta tsaya ba. A sauran kananan biranen Russia ma jama'a sun fito don nuna adawar su da sakamakon zaben.

Amma yayinda wasu 'yan kasar ke zanga zanga a bisa zargin magudin zabe, a cewar hukumar zaben kasar, zkomai ya gudana cikin adalci, kuma ta gamsu da sakamkon zaben

Karin bayani