An cimma matsaya a taron da ake yi kan sauyin yanayi

Taro kan sauyin yanayi a birnin Durban na Afirka ta Kudu Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An cimma yarjejeniya a taron da ake yi kan sauyin yanayi

Shugabar taron majalisar dinkin duniya kan sauyin yanayi dake gudana a Kasar Afrika ta Kudu, ta ce an cimma yarjejeniya kan yadda za a bullo wa matsalar fitar da iska mai gurbata muhalli nan gaba.

Shugabar wadda har wa yau ita ce ministar harkokin wajen Afrika ta Kudu ta ce daga karshe wakilai a wajen taron sun amince a kan kalmomin da za a yi amfani da su wajen rubuta yarjejeniyar.

Wakilan Tarayyar Turai da na Kasar India, duk sun yi maraba da sanarwar.

Sai dai wani wakilin Kasar Rasha ya ce bai gane abinda aka cimma matsaya a kai ba, kuma yana bukatar ganin batun a rubuce.

Karin bayani