Yau ake zaben 'yan majalisa a Ivory Coast

Shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Za a gudanar da zabe a Ivory Coast

A yau ne al'ummar Ivory Coast za su kada kuri'a a zaben Kasa baki daya na farko, tun bayan zaben Shugaban Kasar da aka gudanar shekara guda da ta gabata, wanda ya haddasa rikici na tsawon watanni.

Manyan abokan hamayya dai sun hada da jam'iyyar Shugaba Alassane Ouattara da kuma magoya bayan wanda ya gabace shi Laurent Gbagbo, wanda kin saukar sa daga kan karagar mulki ya janyo tashin hakali a Kasar.

Jam'iyyar Mr. Gbagbo dai ta ce za ta kaurace wa zaben.

An dai kai Mr. Gbagbo kotun hukunta laifukan yaki da ke Hague don fuskantar tuhumar aikata laifukan cin zarafin bil'adama.

Daruruwan magoya bayansa ne dai suka yi zanga-zanga a harabar kotun don nuna adawar su da shari'ar da ake yi masa.

Karin bayani