Nick Clegg ya soki matakin David Cameron

Hakkin mallakar hoto PA

Mataimakin Firaministan Biritaniya, Nick Clegg, ya ce sam bai yi murna da sakamakon taron Kolin Tarayyar Turai na ranar Jumma'a, inda Firaminista, David Cameron, ya hau kujerar na ki a kan cimma yarjejeniya game da dimbin bashin da ake bin kasashen da ke amfani da kudin Euro. Sai dai duk da haka, Mr Clegg ya ce jam'iyyarsa ta Liberal ba za ta fita daga cikin gwamnatin hadakar da ita yanzu ba da jam'iyyar Conservative.

Ya ce, "Zai fi zama aibu a kanmu a matsayin kasa idan gwamnatin hadin gwiwar ta wargaje. "Hakan zai haifar da bala'i ga kasar ta fuskar tattalin arziki a wannan lokaci da ake fama da gagarumin rashin tabbas a kan tattalin arzikin." Firaminista Cameron ya ce ya ki sanya wa yarjejeniyar hannu ne saboda ba za ta biya muradun Biritaniya ba.

Mataimakin Firaministan ya ce kalaman na sa ba alama bace da ke nuna cewa gwamnatin gamin gambizar kasar ta tasanma wargajewa ba, yana mai cewa ai idan kowa ya kama gabansa yanzu to kasar zata shiga wani mawuyacin hali.

Sai dai kuma a wani sako ga David Cameron da kuma jami'iyyar masu ra'ayin mazan jiya, Mr Clegg ya ce zai yi duk iyawar sa wajen ganin cewa Biritaniya bata ware kanta daga tarayyar turai ba.

Karin bayani