Mutum guda ya mutu a Jos na Najeriya

Tashin hankali a Jos, babban birnin jahar Filato
Image caption Wasu bama-bamai sun tashi a Jos, babban birnin Jahar Filato

Hukumomi a jihar Filaton Nijeriya sun yi karin haske a dangane da tashin bama-bamai guda uku jiya da dare, a wasu gidajen kallo a Jos babban birnin jihar.

Hukumomin dai suka ce mutum guda ne ya rasa ransa wasu karin goma sha shida kuma suka samu raunuka.

Jihar Filaton dai na daya daga cikin jihohin Nijeriya da suk fi fuskntar matsalolin tsaro, inda dubban mutane suka rasa rayukansu a tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini da kuma siyasa a yan shekarun nan.

Bama-baman dai sun tashi ne a wasu wurare guda uku da suka hada da mahadar hanyar Fina da kuma wani wuri da ake cewa Odus da wata hanya ta bayan gari dake danganawa zuwa Jahar Bauchi wato Ring Road a turance

Kakakin gwamnatin Jahar Filato ya tabbatar wa da BBC tashin bama-baman, kuma yace gwamnatin Filaton ta damu matuka

Bayanai dai sun nuna cewar bama-baman sun tashi ne da kusan karfe 10 na daren jiya, agogon Najeriya

Wakilin BBC a Jahar Filato yace jama'a sun kwana cikin zulumi da kuma fargaba tun daga sannan

Jahar Filato dai ta jima tana fama da tashe-tashen hankula dake da nasaba da addini da kabilanci da kuma siyasa

Karin bayani