Rashin aikinyi ya shiga cikin manyan matsaloli

binciken bbc
Image caption binciken bbc

Sakamakon wani bincike da BBC ta gudanar ya nuna cewa, batun rashin aikin yi ya shiga sahun sauran manyan matsaloli kamar cin hanci da rashawa da kuma talauci wadanda duka ke cikin jerin abubuwan da ke damun jama'a a kasashe da dama.

Kusan kashi biyar cikin dari na wadanda aka yiwa tambayoyi yayin binciken a kasashen da ke tasowa da wadanda suka ci gaba sun ce suna tattauna matsalar rashin aikin yi a 'yan watannin nan.

Adadin ya ribanya har sau shidda, idan aka kwatanta da irin wannan bincike da BBC ta gudanar a shekarar 2009.

Manyan batutuwanda ake tattaunawa a kai sun banbanta a kasashe 23 da aka gudanar da binciken, tattalin arziki shine muhawarar da yan kasashen Amurka da Faransa da Japan suka fi yi, yayinda cin hanci da rashawa ne batun da yan Nigeria da Misra da India suka fi tabka mahawara a kai.