CDS Rahama ta ce lallai a yi bincike

niger
Image caption taswirar niger

Kwamitin zartarwar jami'iyar CDS Rahama a jamhuriyar Niger, ya yi kira ga shugaban kasar da gwamnatinsa da su gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da gaskiya a game da zanga zangar da aka yi kwanaki 3 a jere ana yi a Damagaram.

Zanga zangar dai ta haddasa mutuwar mutane biyu tare da kona wani ofishin 'yan sanda da wani banki.

Kwamitin zartarwar na CDS Rahama ya yi wannan kira ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa bayan wani taro da ya yi domin yin nazari a kan yadda yake ganin al'amurran kasa na tafiya.

Sai dai kuma tun faruwar rikicin na Damagaram gwamnatin ta Nijar ta ce, za ta yi bincike domin gano wadanda ke da hannu a mutuwar mutanen 2 cikin zanga-zangar.