'Yan sanda a Najeriya sun hallaka dubban mutane'

'Yan sandan Najeriya Hakkin mallakar hoto google
Image caption 'Yan sandan Najeriya

Wata kungiya mai zaman kanta a Nigeria ta fidda sakamakon wani bincike da ta ce ta gudanar a kasar, wanda ke nuna cewa dubban mutane ne suka rasa rayukansu a kasar, a hannun 'yan sanda, daga shekarar 1999 zuwa 2011. Kungiyar mai suna Intercity Society, ta kuma ce a wannan tsakanin, kudaden da 'yan sanda suka karba a wurin jama'ar kasar a matsayin na goro, ya kai naira miliyan dubu 54.

Rundunar 'yan sandan Najeriyar ta yi watsi da sakamakon binciken.

Karin bayani