BBC navigation

Wani matashi ya kai hari a Belgium

An sabunta: 13 ga Disamba, 2011 - An wallafa a 19:51 GMT
Harin da aka kai a Liege na kasar Belgium

Harin da aka kai a Liege na kasar Belgium

Wani mutum ya bude wuta da bindiga, kana ya jefa nakiyoyi daga rufin wani gini, inda ya halaka mutane uku kafin ya kashe kansa, a wata kasuwa dake cike da masu sayayyar kirsimati, a birnin Liege na kasar Belgium.

Akwai wasu mutanen su saba'in da biyar da suka jikkata, wasu daga ciki munanan raunuka.

Yansanda sunce, suna daf da yiwa maharin tambayoyi kafin hawa kan rufin wani gini a tsakiyar Liege.

Daga nan kuma sai ya jefa gurneti sannan ya yi harbi kan taron jama'a a Kasuwa, kafin ya kashe kansa.

Mai gabatar ka kara ta birnin Liege, Daniele Reynders ta ce wanda ya kai harin, ana kiransa Nurudin Amrani, da aka haifa ranar 15 ga watan Nuwamban 1978.
Kuma shi kadai ya kai harin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.