Wani bom ya yi barna a garin Maiduguri

Wani bom ya yi barna a garin Maiduguri Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An sha kai hare-hare a garin na Maiduguri

Wani shirgegen bam da kuma harbe-harben bindiga sun yi mummunar barna a garin Maiduguri na jihar Borno - cikin wadanda abin ya ritsa da su har da sojoji.

Rundunar samar da tsaro ta hadin gwaiwa JTF dai ta tabbatar da afkuwar lamarin da cewar maharan biyu wadanda take zargin 'yan Kungiyar Boko Haram ne na cikin wata mota mai kirar Golf lokacin da suka kai harin kan jami'ansu a unguwar London Ciki.

Haka kuma ta kara da cewar mutum guda ya mutu nan take yayin da daya ya tsere.

Sai dai rahotanni na cewa mutanen da suka mutun sun haura haka, kuma akwai jami'an soji a cikin wadanda suka jikkata.

Mazauna garin sun zargi jami'an rundunar ta JTF da mayar da martani cikin fushi ta hanyar yin harbi kan mai tsautsayi da kuma kona gidaje - da zarar an kai makamantan wannan hari a baya.

'Ba wani gida da aka hara'

Amma mai magana da yawun sojin ya musanta zargin.

"Babu wani mutum da aka kaiwa hari ko wani gida da aka kona," kamar yadda Lieutenant Colonel Hassan Mohammed, na rundunar ta JTF ya shaida wa BBC.

Mazauna unguwar sun ce an ji karar harbe-harben bindiga bayan tashin bam din. Inda suka zargi sojoji da bude wuta kan fararen hula - zargin da sojin suka musanta.

Rundunar sojin ta JFT dai na fuskantar suka kan yadda take gudanar da ayyukanta a Maiduguri, inda wasu dattawan garin ke kiran da a janye sojin kwata-kwata.

Karin bayani