Jonathan ya gabatar da kasafin kudin 2012

Shugaba Jonathan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Jonathan

Shugaba Goodluck Jonathan na Nijeriya ya gabatar da kasafin kudin shekara mai kamawa , bisa hasashen farashin mai dala saba'in kan kowace ganga.

A sakamakon haka, duk wasu rarar kudi da aka samu, sai a zuba su cikin wani asusu na musamman.

A halin yanzu farashin mai yana kusan dala dari ne akan kowace ganga. Shugaba Jonathan ya shaidawa majalisar dokoki cewa kasafin kudin zai kasance wata hanyar da zxata share fagen kyautata tsarin tattalin arzikin kasar.

Ya kuma ce za a rage yawan kudaden da ake kashewa wajen tafiyar da harkokin mulki. Sai dai shugaban bai ambaci batun nann da ake ta cece kuce a kansa ba, na janye tallafi kan man petur.