Majalisar dinkin duniya ta ba da shawarar kai Syria ICC

Masu zanga-zanga dauke da gawa a Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zanga dauke da gawa a Syria

Shugabar hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar dinkin duniya ta ba da shawarar cewa, a gurfanar da Syria a gaban kotun hukunta laifukan yaki ta duniya wato ICC.

Shugabar hukumar, Navi Pillay, ta ba da shawarar ne sakamakon murkushe masu zanga-zangar adawa da gwamnatin kasar Syria ke yi.

Jakadan Syria a Majalisar, Bashar Ja'fari, ya yi watsi da kalaman Ms. Pillay, inda ya ce ba ta yi adalci ba, kuma ba ta yi gaskiya ba a rahoton da ta gabatar a gaban kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniya.

Shi kuwa Jakadan Birtaniya a Majalisar, Mark Lyall ya shaidawa manema labarai cewa, rahoton da ta gabatar ya tayar musu da hankali.