Rikici kan mallakar fili ya kara kamari a China

Masu zanga zanga a garin Wakun na China Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga zanga a garin Wakun na China

Hukumomin kasar Sin sun rufe hanyoyin shiga wani kauye dake lardin Guangdong, inda zanga zanga kan damar mallakar filaye ke kara tsananta, bayan mutuwar wani mutumin kauyen a hannun 'yan sanda.

Malcolm Moore wani dan jarida ne a kauyen mai suna Wukanya ce wani sabon abu a wannan lamari shi ne cewar, an kori dukkan jami'an gwamnati dake kauyen

Ya kuma ce, an fatattaki dukkan 'yan snadan dake cikinsa.

Mazauna kauyen na Wukan sun ce an hana shigar da galibin abincin da suke bukata.

Wasu hotuna da aka sa a intanet na nuna dubban mutane rike da alluna suna zanga zanga.

Mazauna kauyen na zargin jami'an gwamnati ne da wawurar filayen, suna kuma bukatar gwamnatin kasar ta sa baki.

Karin bayani