Ana zaman makoki a Florence na Italiya

'Yan asalin Senegal a Italiya
Image caption 'Yan asalin Senegal a Italiya

A birnin Florence na Italiya ma ana can ana juyayi, bayan da wani dan bindiga a jiya ya bude wuta kan wasu mutane, a harin da aka bayyana da cewar yana da nasaba da bambancin launin fata.

An sassauto da tutoci kasa kasa, an kuma bukaci shaguna su rufe na tsawon minti goma da tsakar rana.

Wasu 'yan kasar Senegal biyu masu sayar da kaya a kan titi ne aka kashe, aka kuma raunata wasu uku, lokacin da dan bindigar, Gianluca Casseri, ya bude wuta a wata kasuwa dake arewacin birnin.

Daga baya an tsinci gawar Mr Casseri, bayan da ya kashe kansa.

Shugaban Italiya, Giorgio Napolitano ya yi tir da kisan, yana cewar kiyayya ce ta bai gaira ba dalili, da ya zama wajibi hukumomi su yaka.

Karin bayani