Ana yin zagaye na biyu na zaben yan majalisar dokoki a Masar

zaben Masar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption zaben Masar

Yayinda ake zaben majalisar dokoki zagaye na biyu a Masar, jam'iyyu masu ra'ayin Islama na fatan jaddada nasarar da suka samu a zagayen farko .

Tun da sanyin safiya jama'a suka fita suka kafa dogayen layuka.

Zaben na yau ana gudanar da shi ne galibi a yankunan karkara kamar yankin fadamun Nilu, yankin da ake yi ma kallon masu kishin Islama na da karfi.

Wani dan kasar ta Masar, Tarek Al Hawary ya ce, yana fatan a wannan majalisa za a samu wakilci daga dukkan bangarorori, domin al'umar kasar.

Wakilin BBC na cewa zaben ya wuce takara tsakanin masu kishin Islama da masu ra'ayin raba adini da siyasa, ya koma tsakanin bangarori daban daban na masu kishin Islamar.

Yan takara a jamiyyun masu raayin yanci, ba su tabuka wani abin kirki ba a zaben, inda suke a matsayi na ukku.

Banbancin dake tsakanin jamiyyar yan uwa musulmi da yan Salafiyyun na da muhimmanci, domin yan uwa musulmin sun nuna kansu a matsayin masu matsakaicin raayi. To amma a bangare guda yan Salafiyyun ba su da wani sassauci, saidai kuma suna da alaka da talakawan kasar Misra.