An samu karuwar yara da Polio ta kama a Najeriya-UNICEF

Ana digawa wata yarinya allurar Polio Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana digawa wata yarinya allurar Polio

Asusun Kula Yara na Majalisar Dinkin wato UNICEF, ya bayyana cewa yawan yara da suka kamu da cutar shan-Inna, watau Polio ya ninka fiye da sau biyu a Nijeriya a cikin shekara guda.

Asusun na UNICEF, ya ce yara kamar shirin da biyu ne suka kamu da cutar a shekara ta 2010, amma kuma a bana izuwa ranar biyu ga wannan wata na Disamba, an gano yara arba'in da bakwai da suka kamu da ciwon na shan-Inna, kuma lamarin ya fi kamari ne a jihohin Kano da Jigawa da kuma Borno.

To sai dai kuma asusun na UNICEF ya ce an samu raguwar da ake nuna wa allurar rigafin ciwon na Polio, galibi kuma a sakamakon fadakarwa daga bangaren malaman addinai da kuma sarakunan gargajiya.

Asusun na UNICEF ya yi wadannan bayanan a lokacin wani taron manema labarai da ya kira a garin Bauchi.

Karin bayani