An bada shawarar yin raba daidai na sabbin jihohi

Nigeria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Nigeria

Kungiyar Ohaneze ta al'ummar Igbo a Nigeria ta bada shawarar cewa a yi raba daidai wajen kirkiro da sabbin jihohi a tsakanin shiyyoyi shida da ake da su a kasar.

Shawarar na zuwa ne, yayinda ake jiran martanin majalisar dokokin kasar game da batun kirkiro da sabbin jihohi a Nigeriar.

Cif Nduka Eya, babban magatakardan kungiyar ta Ohenze Ndigbo, ya ce kungiyar ta su, ta na bukata ne a sami daidaiton adadin jihohi a tsakanin shiyyoyi shida da ake da su a kasar.

To saidai masana irin su Dokta Abubakar Umar Kari na jami'ar Abuja, suna ganin da wuya wannan shawara ta kai labari, saboda banbancin da ke tsakanin bangarorin kasar.