An tsare Zainab Alkhanawaji

Wasu mata masu zanga-zanga a Bahrain Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu mata masu zanga-zanga a Bahrain

Rahotanni daga Bahrain sun ce an tsare Zainab Alkhawaji, wata `yar rajin kare hakkkin biladama, wadda ke da shafin fadi-ra`ayinka na internet, a wata zanga-zangar da aka yi a kan babban titin da ya dangana da fadar gwamnatin kasar, Manama.

Takwarorinta `yan rajin kare hakkin bil`adama sun yi kira da a gaggauta sako ta.

Wadanda aka yi abin a kan idanunsu sun ce jami`an tsaro sun yi amfani da barkonon tsohuwa da gurneti wajen tarwatsa daruruwan mausu zanga-zangar da ke adawa da gwamnati.

Wannan lamari dai ya auku ne a daidai lokacin da jekadan da ke kula da hakkin bil`adama na kasar Amurka, Michael Posner ke wata ziyara a kasar.

Wakilin BBC ya ce Zainab Alkhawaji diyar wani fitaccen dan adawa ne da aka yi wa daurin rai-da-rai bayan wata zanga-zangar da aka yi a watan Fabarairu, inda aka tuhume shi da shirya juyin mulki.

Karin bayani