An samu Jacques Chirac da laifin cin hanci

Mr Jacques Chirac, Tsohon Shugaban Faransa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Jacques Chirac, Tsohon Shugaban Faransa

An samu tsohon shugaban kasar Faransa, Jacques Chirac da laifin cin hanci da rashawa, bayan wata shari'a da aka dade ana yi.

An samu tsohon shugaban ne da laifin yin almubazzaranci da kuma cin amana, bayan da ya kirkiro wasu guraben aiki na bogi ga wasu yan jam'iyyarsa a lokacin da ya ke rike da mukamin magajin garin birnin Paris.

Wakilin BBC ya ce Mr Chirac bai halarci zaman kotun ba, domin yana fama da mummunan ciwon mantuwa, to amma diyarsa na cikin kotun, inda ta saurari hukuncin da alkali ya yanke.

Wannan kuma hukunci ne da ya kara jaddada 'yancin bangaren shari'a na kasar.

An dai yankewa Mr Chirac, hukuncin daurin jeka ka gyara halinka ne na tsawon shekaru biyu.

Karin bayani