Fyade a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ya kazanta

Fyade a Congo
Image caption Fyade a Congo

Shugabannin kasashen yankin Afirka da tabkin Great Lakes ya ratsa ta cikinsu za su yi wani taro a yau a kasar Uganda, don tattaunawa kan matsalolin tsaro da fyade.

Cin zarafi ta hanyar lalata, shine daya daga cikin manyan matsalolin da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ke fuskanta, inda rahotanni ke nuna cewa an yiwa mata da dama fyade.

Yawancin lokuta, gungun yan bindiga ne kan aukawa mata da fyade, a wasu lokutran ma, su halaka su. Yara kanana ma ba su tsira ba.

Wani bincike ya nuna cewa kashi 12 cikin dari na mata a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo an yi masu fyade a kalla sau guda, kuma alamarin bai tsaya a yankunan da ake yaki kadai ba.

Abu mafi tada hankali kuma shi ne, wasu daga cikin wadanda suke yin fyaden, babu wata damuwar da suke nunawa, wanda ke nuna cewa, idan suka samu sarari, za su iya kara aikatawa.