NLC ta yi barazanar yin zanga-zanga a Najeriya

Wasu ma'aikata dake zanga-zanga a Najeriya Hakkin mallakar hoto b
Image caption Wasu ma'aikata dake zanga-zanga a Najeriya

A Najeriya, Kungiyar kwadagon kasar na barazanar shirya zanga-zanga don kalubalantar gwamnatin tarayya game da rashin sanya tallafin man fetur a cikin kasafin kudin kasar na badi.

Kungiyar ta NLC dai ta ce janye tallafin man zai jefa al`umma cikin wahala saboda haka za ta yi bakin kokarinta wajen tirsasa wa gwamnati domin ta sauya shawara.

Sai dai a nata bangaren, gwamnatin Najeriyar ta ce tana baiwa kungiyar kwadagon hakuri saboda ba za ta yi abin da ya fi karfinta ba, amma kungiyar ta NLC ta ce bada hakuri bai isa ba.

A cikin wannan makon ne dai shugaban Najeriyar, Goodluck Jonathan ya gabatarwar majalisun Tarayyar kasafin kudin na badi domin yin muhawara a kai, amma wasu daga cikin 'yan majalisun sun ce ba za su yarda a cire batun tallafin man daga kasafin kudin ba.

Karin bayani