Manoma a Nigeria, na barazanar watsi da noma auduga

noman auduga
Image caption noman auduga

Manoman auduga a Najeriya na barazanar daina noman audugar, muddin hukumomin kasar ba su sauya halayyarsu dangane da noman na auduga ba.

Yanzu haka dai manoma na noma audugar mai yawan gaske, amma kuma babu masu saya, saboda durkushewar masana'antu masu amfani da auduga.

Hukumomi a Nigeria dai na cewa sun himmatu domin taimakawa manoman ta hanyar farfado da masaku da kuma magurzan auduga a kasar da nufin karfafa gwiwar manoman.

To saidai da alamu, har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.