An yi artabu da wasu 'yan boko haram a Kano

Jami'an tsaro a Nigeria
Image caption Jami'an tsaro a Nigeria

A Kano, mutane akalla hudu sun rasa rayukansu, a wata musayar wuta da aka yi tsakanin 'yan sanda da wasu da ake zaton 'yan Boko Haram ne, a kusa da makarantar 'ya'yan mayakan rundunar sojan saman Najeriya, a kauyen Kwa.

Rahotanni sun kuma ce, an jiwa daya daga cikin maharan rauni, kuma yanzu haka yana hannun jami'an tsaro.

An kuma ce, an yi harbe harbe a wata unguwa da ke wajen birnin Kanon, bayan da mazauna unguwar suka tsegunta wa jami'an tsaro kasancewar wasu bakin da basu yarda da su ba.

An kuma kama kaset-kaset da dama na marigayi Muhammad Yusuf, tsohon shugaban Boko Haram, da kuma na sabon shugaban kungiyar Malam Shekau.

An kuma gano makaman gargajiya da abubuwan hada bam

Karin bayani