An yankewa Carlos Jackal hukuncin daurin rai da rai

''Carlos the Jackal'' Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An yankewa ''Carlos the Jackal'' hukuncin daurin rai da rai

An yankewa wani mai tsatsauran ra'ayi da aka san shi a duk fadin duniya wanda ake kira 'Carlos the Jackal' hukuncin daurin rai da rai a Faransa bayan hare haren bama-bamai da ya kai a shekarun 1980.

Carlos wanda sunansa na asali -Ilich Ramirez Sanchez dama dai yana garkame ne a gidan kaso a Faransan saboda harin da ya kai, wanda kuma ya haddasa mutuwar mutane uku a shekarar 1975.

An dai samu karin hujjojin da ke nuna hannunsa akan harin bam din daya kashe mutane 11 a Paris da Marseille.

Jim kadan bayan da aka yanke masa hukunci, daya daga cikin lauyoyin da suka gabatar dashi gaban kuliya Jacques Miquel yace ''kotu ta yi Allah wadai da Ramirez Sanchez da abokansa biyu zuwa daurin rai da rai, tare da daurin shekaru 18 akan Ramirez ba tare da ya motsa ko nan da can ba''.

Karin bayani