Etienne Tshisekedi ya ce za'a rantsar da shi a matsayin shugaban kasa

Hakkin mallakar hoto

Jagoran 'yan adawar da ya sha kaye a zaben shugaban kasar da aka yi a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, Etienne Tshesikedi, ya ce za'a rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a wannan makon.

Etienne Tshesikedi ya ce za'a rantsar da shi ne duk da hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na cewa shugaba mai ci Joseph Kabila ne ya yi nasara a zaban. Ranar juma'ar da ta wuce ne kotun ta bayyan cewa Joseph Kabila ne ya lashe zaban da kusan kashi arba'in ta tara cikin dari da kuri'un da aka kada, yayain da shi kuma Mr Tshisekedi ke da sama da kashi talatin cikin dari kawai. Mr Tshisekedi dai ya ce har yanzu shi yana daukar kansa a matsayin zababban shugaban kasar Congo.

Karin bayani