Kotu ta bai wa CPC gaskiya a Katsina

Muhammadu Buhari na  jam'iyar  CPC Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Muhammadu Buhari na jam'iyyar CPC

A Nigeria, kotun kolin kasar ta baiwa Jam'iyyar CPC gaskiya a karar da ke gabanta kan takaddamar da ake yi dangane da batun yan takara na wasu kujerun majalisar dattawa da majalisar wakilai daga Jihar Katsina.

Kotun ta bayyana cewar kotuna suna da iyaka akan irin bakin da zasu iya tsomawa akan duk wani rikici na cikin-gida na Jam'iyyu.

Ana dai takaddama ne akan kujerun a sakamakon zabubbukan fitar da gwani biyu da aka yi gabanin zaben watan Aprilu, inda uwar Jam'iyya ta gabatar da 'yan takararta yayin da wani bangare, karkashin Senator Lado Dan-Marke, suka gabatar da wasu jerin sunayen, wadanda kotun tarayya ta ce su ne suka cancanta.

Fassarar da wasu ke baiwa hukuncin dai shi ne cewar, uwar jam'iyar ta CPC ce ke da ikon mika sunayen 'yan takara ga hukumar zabe.

Karin bayani