Tsohon shugaban kasar Czech, Vaclav Havel ya rasu

Hakkin mallakar hoto Reuters

Allah ya yi wa tsohon shugaban kasar Czech, rasuwa yana da shekaru saba'in da biyar

bayan ya sha fama da rashin lafiya. A shekaru 1970 ne Havel yai suna a idon duniya a matsayin mai sukar gwamnati a wasannin kwaikwayon da yake rubutawa. Shi ne ya shirya zanga-zangar lumana na juyin-jaya halin da akai tayi wanda aka fi sani da Velvet Revolution, wanda ya kawo karshen tsarin kwaminisancin a Czechoslovakia a shekarar 1989. An zabe shi a matsayin shugaban kasa ya kuma ci gaba da aiki har tsawon shekaru goma sha ukku inda ya yi ta sa ido kan shigar kasar sa kungiyar tarayyar Turai.