'Yan jam'iyyar adawa a Iraqi sun fice daga zauren majalisar dokokin kasar

Hakkin mallakar hoto AFP

'Yan babbar jam'iyyar adawa a Iraqi sun fice cikin fushi daga zauren majalisar dokokin kasar domin nuna kin amincewar su da suka kira kakagidan da Praminista, Nouri al-Maliki ke yi wajen yanke shawara kan al'amuran kasa. Jam'iyyar Iraqiyya mai akidar raba addni da siyasa ta tsohon Praministan kasar, Iyad Allawi ta jefa kasar cikin rikicin siyasa, kwanaki kadan bayan janyewar dakarun Amurka daga Iraqin.

Jam'iyyar wadda ke da kashi daya cikin hudu na kujerun majalisar dokokin ta yi kiran da a zauna kan teburin shawara da gwamnati kasar da 'yan Shi'a ke jagoranta.

Karin bayani