An kashe masu zanga zanga a Kazakhstan

masu zanga zanga a Kazakhstan Hakkin mallakar hoto
Image caption masu zanga zanga a Kazakhstan

Rahotanni daga Kazakhstan sun ce an yin arangama tsakanin masu zanga-zanga da sojojin gwamnati a wani gari dake Yammacin kasar.

Rahotannin sun ce 'yan sanda sun bude wuta a kan dubban ma'aikatan hako man fetur, da ke zanga-zanga a babban dandalin dake tsakiyar garin Zhanao-zen, suna masu kokawa da karancin albashinsu da kuma korar wasu abokan aikinsu da aka yi.

Wadanda suka shaida al'ammarin da idanunsu, sun ce an kashe masu zanga-zangar da dama, wasu karin kuma sun samu raunuka.

Wakiliyar BBC ta ce shaidun sun ce an cinnawa wasu gine-gine dake kewayen dandalin, wuta, ciki har da ofisoshin gwamnati da wani otel da kuma Hedkwatar kamfanin mai na kasar.

Yanzu haka dai gwamnati ta tura wasu karin zaratan sojoji don kwantar da tarzomar.

Sai dai hukumomin Kazakhstan din sun musanta cewa jami'an tsaro sun yi harbi a kan masu zanga-zangar.

Karin bayani