Isra'ila ta saki rukunin karshe na fursunoni Palastinawa

Hakkin mallakar hoto AFP

Isra'ila ta saki rukunin karshe na fursunoni Palasdinawa su dari biyar da hamsin.

Sakin dai shine zagaye na biyu kuma na karshe na yarjejeniyar da suka kulla domin tabbatar da sakin sojin Isra'ila, Gilad Shalit, bayan ya kwashe shekaru biyar a tsare a Gaza. A wannan karon ba wani bakin ciki ko rudani game da sakin pursunonin kamar yadda aka samu a zagayen farko. Jami'an Isra'ila sun ce duka wadanda za'a sakin ba wanda aka yanke wa hukuncin kisa.

Karin bayani