Wammako ya lashe zaben fidda gwani

Gwamnan jihar Sokoto a arewacin Najeriya, Aliyu Magatakarda Wammako ya lashe zaben fidda gwamni na jamiyyar PDP mai mulkin kasar.

Hakan na nufin shi ne dan takarar jamiyyar, a zaben gwamnan da za'a gudanar a jihar a watan Maris

Sai dai biyu daga cikin mutane ukkun dake takara a zaben sun kaurace masa.