An dage takunkumin da aka sanyawa Babban Bankin Libya

Banki a Libya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An dage takunkumin da aka sanyawa babban bankin Libya

Majalisar Dinkin Duniya ta dage tukunkumin da ta sanyawa babban bankin Libya, abinda zai baiwa sabuwar gwamnatin Kasar damar ikon gudanar da dubban miliyoyin kadarorin Kasar dake Kasashen waje.

Sabuwar gwamnatin Libya dai ta jima tana kamun-kafa a sakarmata wadannan kudaden, saboda a cewarta kudaden nada muhimmanci wajen daidaita tattalin arzikin Kasar.

Matakin na Majalisar Dinkin Duniya ya janyo su ma Kasashen Amurka da Burtaniya sun janye takunkuminsu akan dukiyar Libyar dake Kasashensu.

An yi kiyasin cewar ana rike dala biliyan dari da hamsin na irin kadarorin Kasar dake Kasashen waje a lokacin yakin basasar Kasar

Sannan bayan kifar da gwamnatin Mu'ammar Gaddafi, an ki sakin kudaden saboda babu tabbas ko wadanda ke jan-ragamar Kasar suna da hadin kan da zasu iya tafiyar da dukiyar.

Karin bayani