'Yan adawar Syria na taro a Tunisia

Zanga-Zanga a Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan adawar Syria na taro a Tunisia

Babbar kawancen adawa ta Syria wato Syrian National Council na taro a Tunisia a yau, shekara guda bayan tarzomar data janyo juyin-juya hali a Kasashen larabawa.

Akalla wakilai 200 ne yawancin 'yan boko dake zaune a Kasashen waje ne ke halatar taron, inda ake sa ran zasu cimma matsaya akan yadda zasu bayyana kansu a matsayin gwamnati mai jiran gado, don maye gurbin Shugaba Assad.

Taron nasu na zuwa ne daidai lokacin da ake gudanar da zanga-zanga a Syria

A jiya juma'a masu zanga-zanga sun yi jerin gwano don ganin an dauki kwararan matakai akan Syria.

Karin bayani