Dakarun Amurka na karshe na ficewa daga Iraqi

Sojin Amurka a Iraqi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Amurka na karshe na ficewa daga Iraqi

Dakarun Amurka na karshe dake ficewa daga kasar Iraqi sun ketara zuwa Kasar Kuwait, abinda ke kawon karshen mamayar da Amurka tayi a Iraqin na tsawon shekaru kusan tara da hambarar da Marigayi Saddam Hussein.

Tun a bara ne dai sojojin Amurka suka daina kai hare-hare, inda suka mika ragamar aikin ga sojojin Iraqi.

Akalla sojojin Amurka 4,500 ne suka mutu sannan wasu dubun-dubatar 'yan Iraqi suma suka rasa rayukansu tun lokacin da Amurka ta jagoranci yakin a shekara ta 2003, sannan Amurkar ta kashe kusan dala tiriliyan daya a yakin.

Yayinda akasarin 'yan Iraqin su kai imanin cewar lokaci ya yi na Amurkawan su tattara ina-su ina-su su bar Kasar, sai dai wasu da dama kuma na cikin damuwa game da kalubalen da suke tunanin za'a fuskanta a nan gaba

Karin bayani