Zaben fidda dan takarar Gwamna a Sokkoto ya bar baya da kura

Taswirar Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Abokan hamayyar Gwamna Wammako na Sokkoto sun yi watsi da sakamakon zaben sa

A Najeriya, abokan hamayyar Gwamna Aliyu Wamakko a zaben fitar da dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP da aka yi jiya a Sokkoto, sun yi watsi da sakamakon zaben da ya baiwa gwamnan nasara, suna masu cewa zaben ba shi da inganci.

Dr. Mahe Dange shine shugaban kwamitin yakin neman zaben Sanata Abubakar Gada, ya kuma shaidawa BBC cewar za su daukaka kara kamar yadda doka ta tanada

Ya kara da cewar basu gamsu da yadda zaben ya gudana ba, a saboda haka ne ma yasa yace suka kauracewa dandalin da aka gudanar da zaben.

Sai dai kuma Alhaji Ikira Aliyu Bilbis wanda shine shugaban kwamitin da shedikwatar jam'iyyar shiyyar arewa maso yamma ta turo domin sa ido akan yadda zaben ya gudana ya yi watsi da wannan batu, yana mai cewar zaben fidda dan takarar gwamnan ya inganta

Sakamakon zaben dai ya zowa masu sharhi kan al'amurran siyasa da dama a Kasar da mamaki, ganin yadda suka yi hasashen cewar akwai alamun jam'iyyar ba za ta baiwa gwamna Aliyu Wammako damar tsayawa takara a zaben ba, kamar yadda tayi wa gwamnan jahar Bayelsa Timiprey Silva a watan daya gabata.

Karin bayani