Shugabar IMF na ziyara a Najeriya

Shugabar IMF, Christine Lagarde Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugabar IMF, Christine Lagarde na ziyara a Najeriya

Ranar Litinin Shugabar Hukumar ba da Lamuni ta Duniya IMF, Christine Lagarde, za ta gana da Shugaban Najeriya Dr. Goodluck Jonathan da ministar kudin kasar, Dr Ngozi Okonjo Iweala, da kuma Shugaban babban Bankin kasar, Sanusi Lamido Sanusi a Abuja.

A ranar Lahadi ne Christine Lagarde ta iso Najeriya don yin wata ziyarar aiki.

Masu lura da al'amuran tattalin arziki dai na ganin ziyarar Shugabar IMF ba za ta rasa nasaba da shirye-shiryen da gwamnatin Najeriya take yi ba wajen janye tallafin mai.

Batun janye tallafin man fetur a Najeriya dai na cigaba da janyo kace-nace a Kasar.

Wannan dai ita ce ziyararta ta farko zuwa nahiyar Afirka tun lokacin da ta kama aiki a matsayin shugabar Hukumar ta IMF.

Haka kuma Shugaban na Najeriya zai karbi bakwancin Shugaban Kasar Chadi Idris Deby.

Karin bayani