Shugaban Koriya ta Arewa ya mutu

Marigayi Shugaba Kim Jong-il na Koriya ta Arewa Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Shugaba Kim Jong il ya rasu yana da shekaru 69 a duniya

Gidan talabijin din Kasar Koriya ta Arewa ya sanar da mutuwar Shugaban Kasar, Kim Jong- Il.

Wata mai gabatar da labarai sanye da bakaken kaya ce ta sanar da mutuwar Mr Kim, inda ta yi ta sharbe hawaye.

Kamfanin dillancin labaran Kasar ya ce Kim Jong-Il mai shekaru 69 ya mutu ne sakamakon bugun zuciya a cikin wani jirgin kasa a ranar Asabar.

Dama dai ya jima yana fama da rashin lafiya.

Za a yi jana'izarsa

Za a yi jana'izar Kim Jong-Il ne a babban birnin Koriya ta Arewa Pyongyang, a ranar 28 ga wannan watan.

Kim Jong-Il ya gaji mulkin Kasar ne a wajen mahaifinsa, Kim Il Sung, wanda ya mutu a shekarar 1994.

Jim kadan bayan an sanar da mutuwar sa ne dai darajar kasuwannin kudade ta fadi.

Nan ba da dadewa ba ne kuma za a gudanar da taron majalisar tsaron kasar.

Tuni rundunar Sojin Kasar ta daura damarar shirin ko-ta-kwana.

Karin bayani