Amurka na son shugabannin Iraqi su hada kai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden

Mataimakin shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya bukaci Fira Ministan Iraqi, Nouri al-Maliki ya yi aiki tare da sauran jam'iyyu don warware rikicin siyasar kasar.

Kiran ya biyo bayan gargadin da mataimakin Fira Minitsan kasar, Saleh al-Mutlaq, ya yi ne cewa kasar na daf da afkawa cikin wani sabon rikicin addini.

Mista al-Mutlaq, wanda shi ne mafi girman mukami a cikin mabiya Sunna na kasar, ya zargi Mista al-Maliki, wanda dan Shi'a ne da hannu a ba da sammacin kama mataimakin shugaban kasar, Tariq al-Hashimi.

Zaman dar-dar din da ake yi a kasar ya zo ne kwanaki kadan bayan Amurka ta janye dakarunta daga kasar.

Joe Biden ya bukaci shugabannin kasar Iraqi da su yi aiki tare domin gujewa afkawa cikin wani sabon rikicin bangaranci a kasar.

Biden ya nuna damuwa

Fadar White House a Amurka ta ce Mista Biden ya nuna damuwarsa ne a wata hira da su ka yi da Fira Ministan Iraqi, Nouri al-Maliki, ta wayar tarho, bayan da Fira Ministan ya ba da sammacin kame mataimakin shugaban kasar, Tariq al-Hashemi, saboda zargin ta'addanci.

Wannan batu dai ya sanya fargabar cewa, gwamnatin hadin gwiwa a kasar na iya wargajewa wasu 'yan kwanaki bayan da Amurka ta janye dakarun ta a kasar.

Amurka dai ta bayyana bukatar ta ta ganin an samu gagarumin sauyi a Iraqin.

Rikicin da aka yi tsakanin 'yan Sunni da Shia a shekarun dubu biyu da shida zuwa bakwai ya janyo asarar dubban rayuka a kasar.

Jam'iyyar gurguzun 'yan Sunni a kasar na kauracewa Majalisar dokoki da kuma gwamnatin kasar, saboda nuna adawarta da sammacin da aka bayar na kame mataimakin shugaban kasar wanda dan Sunni ne.

Mataimakin Fira Ministan kasar, Saleh al-Mutlak, wanda shima dan Sunni ne ya ce kasar na fuskantar babban rikici.

A yanzu haka Hashemi yana yankin Kurdawan kasar mai zaman kansa, kuma ya musanta duk wani zargi da ake yi masa.

Karin bayani