Lagarde ta kammala ziyara a Nijeriya.

Lagarde da shugaba Jonathan Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugabar IMF, Ms Lagarde da Shuagaba Jonathan na Nijeriya

Asusun bada lamuni na IMF ya ce, Najeriya na da karfin da za ta ci gaba da gudanar da harkokin tattalin arzikinta, saboda haka ba ta bukatar tallafi daga gare shi kuma.

Shugabar Asusun, Christine Lagarde, ita ce ta bayyana haka, a wata tattaunawar da ta yi da `yan kasuwa da kuma kungiyoyin farar-hula a Lagos.

Hakan na zuwa ne yayinda ake zargin ta zo ta shawo kan Nijeriyar ta sake karbar wani bashin daga hukumar.

Wannan tattaunawar dai ita ce hidima ta karshe, a cikin jerin ayyukan da ta yi a Najeriyar, kafin ta wuce zuwa Jumhuriyar Nijar.

A Nijar din, ana sa ran zata gana da hukumomi, domin yin shawarwari, kana kuma zata ziyarci wasu wurare.

Karin bayani