Iraqi ka iya fuskanatar sabon rikici inji Mataimakin Piraminista

Hakkin mallakar hoto AFP

Mataimakin Piraministan Iraqi Dan Sunni, Saleh Al Mutlaq ya ce kasar ka iya afkawa cikin wani sabon rikicin addini saboda matakan da Piraminista Dan Shi'a, ke dauka.

Saleh Al - Mutlaq ya ce, shi da kuma sauran shugabannin yan sunni na jin tsoron irin abunda ya faru da Mataimakin Shugaban kasa, Tareq Al-Hashemi, wanda ke da aka bayar da sammacen kamunsa game da zargin alaka da ta'addanci.

Ya kuma zargi Maliki da kasancewa wanda ya fi Saddam Hussein bakin mulki

A cewar sa : ''Saddam Mutum ne mai mulkin kama karya, Al-Maliki ma mai mulkin kama karya ne. Amma kuma a lokacinsa, Saddam yayi ayyuka masu kyau na gine gine

Amma Al Maliki ya kasa samar da ayyukan komai ga jama'ar sa, da kuma ga kasa.''

A wajen wani taron manema labarai a birnin Irbil, Tareq al-Hashemi dai ya bayyana tuhumar a matsayin wani kitsi.

Wani Kakakin Pirayim Minista Maliki ya bukaci dukanin bangarori da su yi tattaunawa don warware matsalar.

Karin bayani