An kashe mutane biyar a Kagoro, Nijeriya

Matsalar tsaro a Nijeriya
Image caption Matsalar tsaro a Nijeriya

Rahotanni daga Kudancin Kaduna a Nijeriya sun ce, mutane biyar sun hallaka, kuma wasu biyar din na can kwance a asibiti da raunuka, sakamakon wani harin da aka kai a unguwar Rami, a garin Kagoro.

An ce maharan sun je garin Kagoron ne dauke da bindigogi, kuma bayanai sun nuna daga cikin wadanda aka kashen sun hada da maza hudu da mace daya.

Hukumomi a yankin sun tabbatar da aukuwar lamarin, shi ma kwamishinan 'yan sandan jihar , Balah Nasarawa ya tabbatar da aukuwar lamarin ya kuma ce suna gudanar da binccike, amma ba su kama kowa ba.

Tun bayan zaben shugaban Najeriyar na watan Afrilu ake ta fama da rikice-rikice masu nasaba da addini da kuma kabilanci a kudancin jahar Kadunar, inda Krista ke da rinjaye.

Karin bayani