Najeriya ta kaddamar da sabon tauraron dan Adam

Hakkin mallakar hoto NASA
Image caption Tauraron dan adam na Amurka

Najeriya ta kaddamar da sabon tauraron dan Adam a birnin Xichang, na kasar China ranar Litinin.

Tauraron, wanda ake kira NigComSat-1R, a cewar hukumomi, zai taimaka wajen habaka tattalin arzikin kasar, musamman ta fannin sadarwa, da intanet, da kare muhalli da kuma samar da tsaro.

An kaddamar da tauraron ne domin maye gurbin NigComSat-1 wanda ya bace a sararin samaniya a shekara ta 2009.

Dr Bashir Gwandu babban jami'i a Hukumar Sadarwa ta Najeriya, wanda ya halarci bikin kaddamar da tauraron a kasar ta China, ya shaidawa BBC cewa Najeriya ba ta kashe wasu kudi masu yawa ba saboda ta yiwa tsohon tauraron inshora.

Har wa yau ya ce babu tabbas akan sake bacewar tauraron saboda yadda yake kusa da rana.

"Na(tauraro) kasashe da yawa na faduwa saboda zafin rana da nisan da tauraron yake da shi a sararin samaniya, saboda haka bamu san yadda za ta kasance ba," In ji Dokta Bashir Gwandu.