An kashe sojojin da suka so sauya-sheka a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Syria, suna fitowa daga yankin Hama

An ba da rahoton cewa dakarun Syria sun harbe sojojin kasar fiye da saba'in wadanda suka yi yunkurin sauya sheka don su bi sahun masu adawa da Shugaba Bashar al-Assad.

An dai harbe mutanen ne da bindigogi masu sarrafa kansu a lokacin da suke kokarin tserewa daga wani sansanin soji a lardin Idlib.

Masu fafutuka sun ce an kuma kashe masu zanga-zanga farar hula su hamsin a wasu wurare daban.

Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya yi amfani da kaukkausan lafazi don yin Allah-wadai da gwamnatin Syria saboda yadda ta yi amfani da karfi ta murkushe masu adawa da ita, bayan zauren ya amince da wani kudurin da kasar Rasha ta gabatar da gagarumin rinjaye.

Har wa yau rahotanni sun ce sojojin da suka sauya sheka sun kashe sojojin gwamnati uku a yankin Idlib.

Tun da farko dai kasar Syria ta amince da wata yarjejeniya da za ta bar wasu jami'an sa ido daga kungiyar kasashen larabawa shiga kasar domin su ganewa idanunsu abin da ke faruwa a kasar.

Ministan harkokin wajen Syria, Walid Muallem, ya ce kungiyar kasashen labarawa ta amince da gyaran da kasar ta nema ga kudirin da ta zartar na sa ido a kasar.

Kungiyar kasashen larabawa dai ta ce za ta tura wata tawaga kasar a makon nan.