Karin zub da jini a Syria

Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Sojojin da suka sauya sheka a garin Idlib

Rahotanni daga majiyoyin 'yan adawa a Syria sun ce an samu karin zub da jini a kasar, inda sojojin gwamnati suka hallaka sojojin da suka sauya sheka da dama.

Wani mai fafutukar kare hakkin bil'adama ya shaidawa BBC cewa an kashe sojojin da suka sauya sheka da kuma fararen hula sama da dari da hamsin bayan da dakarun gwamnati suka yi musu kawanya a wani kwari.

Har wa yau rahotanni sun ce sojojin kasar da dama ne suka rasa rayukansu.

'Yan adawa a Syria sun ce an kashe mutane da dama a rana ta biyu ta zub da jini da ake yi kasar.

Kungiyar kare hakkin bil'adama a kasar ta Observatory da ke da hedkwata a Landan ta ce an kashe akalla mutane 47, a yayin da kungiyoyin farar hula na cikin gida a kasar ke cewa kusan mutane tamanin ne suka rasa rayukansu.

A yankin arewa maso yammacin kasar, an kashe sojojin da suka sauya sheka da dama, da dakarun gwamnati, da kuma fararen hula a bata-kashin da aka yi a yankin.

Hotunan Video da aka saka a Intanet sun nuna gawar wani yaro da aka raba biyu a cikin tarkacen wasu gidaje biyu da rokokin soji suka sauka a kansa a Homs.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce sama da mutane dubu biyar ne suka rasa rayukansu tun da aka fara zanga-zangar kin jinin gwamnati a watan Mayu.

Gwamnatin Syria dai ta ce tana yakar 'yan ta'adda ne wadanda ke kokarin tayar-da-zaune-tsaye a kasar.

Tashin hankalin ya zo ne kwanaki biyu kawai kafin wata tawagar masu sa-ido ta farko ta isa kasar domin kimanta yanayinta.

Karin bayani