An tsige kakakin majalisar dokokin jihar Kano a Najeriya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

'Yan majalisar dokokin jihar Kano sun tsige shugaban majalisar, Alhaji Yusuf Abdullahi Falgore, a zaman da suka yi na yau.

Sun zarge shi ne da rashin iya shugabanci, tun bayan zaben watan Afrilun bana.

Tuni kuma majalisar ta zabi Gambo Sallau, dan majalisar Kiru, a matsayin sabon shugaban majalisar