An yi musayar wuta da wasu mutane a Sakkwato

Jami'an tsaro a Nijeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jami'an tsaro a Nijeriya

A kalla mutum guda ne ake jin ya mutu a wata musayar wuta tsakanin 'yan sanda da wasu da ake jin 'yan kungiyar nan ceta Jama'atul Ahlus Sunnah Lidda'awati wal jihad ko Boko Haram, a anguwar Mabera dake Sakkwato.

Hakan ya biyo bayan farmakin da 'yan sanda suka kai ne a kan wani gida da ake zargin maboya ce ta 'yan kungiyar.

Mazauna unguwar da lamarin ya auku sun shaidawa BBC cewar sun ji karar harbe-harbe a daren jiya, kafin 'yan sanda su karbe iko da gidan, tare da kama sauran wadanda ke ciki.

Rundunar 'yan sanda a Jihar dai ta tabbatar da yin musayar wutar kuma ta ce tana gudanar da bincike akan lamarin.

A 'yan kwanakin nan, an samu tashin bama-bamai a lokacin da ake hada su, a sassa da dama na arewacin Nijeriyar, lamarin da ya haddasa mutuwar wasu 'yan kungiyar.

Karin bayani