Human Rights Watch tace an kashe fararen hula a Congo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin jami'an tsaro da murkushe masu zanga zanga

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta ce, jami'an tsaro a kasar Jamhuriyar Demkoradiyyar Congo sun kashe akalla fararen hula 24 a kasar a wani yunkuri na murkushe 'yan adawa tun bayan da aka wallafa sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a watan da ya gabata.

A 'yan kwanakin nan dai Shugaban kasar Joseph Kabila wanda ya sake nasarar hawa kujerar shugabancin kasar ya yabawa 'yan sanda da kuma sojoji a kasar a kan yadda su ke tafiyar da harkokin tsaro a kasar.

A wani rahoto da kungiyar Human Rights Watch ta fito da shi, ta ce ta yi hira da mutanen da su ka gani da ido da kuma 'yan uwan wadanda rikicin ya shafa.

Kungiyar ta ce rikici ya barke ne a babban birnin kasar da kuma sauran birane tun bayan da aka bayyana Joseph Kabila a matsayin wanda ya lashe zaben da shugaban kasar da aka gudanar.

Kungiyar ta ce a cikin kwanaki shida ta samu rahotannin da ke nuni da cewa an kashe 'yan adawa ashirin da kuma mutanen da basu ji ba basu gani ba a wasu wurare a birnin kinshasa sannan kuma a kashe mutane hudu a wasu wurare na dabam.

Human Rights Watch ta ce cikin wadanda aka kashe, har da wani yaro dan shekara goma sha uku da haihuwa wanda ke tsaye a kofar gidansu da kuma wata mata da ta fito da duba 'ya'yan ta.

Har wa yau, kungiyar ta yi nuni da cewa an tsare mutane da dama babu gaira ba dalila abun da kuma Kungiyar Amnestt International ta riga ta tabbatar tun a ranar Litinin. Kungiyoyin biyu dai na zargin 'yan sanda ne da kuma sojojin fadar shugaban kasar da yin hakan.

Shugaba Kabila dai ya yi watsi da zargin da ake yiwa jami'an tsaron kasar, inda kuma yake yaba musu saboda yadda su ka tafiyar da al'amuran tsaro, tun bayan da aka kammala zabe a kasar.

Karin bayani