Bama-bamai sun tashi a Iraqi

Image caption Akalla mutane sittin da uku ne suka mutu sanadiyar tashin bama baman

Jami'ai a Iraqi sun ce kimanin mutane sittin da uku ne suka mutu yayin da fiye da mutane dari biyu suka samu raunuka sakamakon tashin wasu bama-bamai a Bagadaza babban birnin kasar.

Ministan harkokin cikin gida na kasar ya shaidawa BBC cewa an kai hare haren ne a wasu wurare goma sha uku a babban birnin kasar.

Kawo yanzu dai babu wasu da suka dauki alhakin kai hare haren da suka abku 'yan kwanaki kafin rukunin karshe na sojojin Amurka su kammala janyewa daga Iraqi.

Haka kuma wadannan hare haren sun abku ne a dai dai lokacin da rikicin siyasa ya barke a kasar bayan da aka bayar da sammacin kame mataimakin shugaban kasar Tareq al- Hashimi, wanda shine dan siyasa mafi girman mukami a tsakanin 'yan siyasa mabiya sunni dake kasar.